Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar NUC ta fitar da sunayen jami’oin da ta amince da su koyar da wasu darussa

Published

on

Hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC ta fitar da sunayen jami’o’in da ta amince sun dinga koyar da darussan da suka shafin digiri na biyu zuwa na uku a fadin kasa baki daya.

 

A cewar hukumar ta ce ta lura da cewar wasu daga cikin jami’o’in kasar nan na bada shaidar kammala karatu a matakin digiri na biyu da na uku wadanda hukumar bata sahale musu ba.

 

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ga manema labarai ta bayyana sunayen jam ‘ion da da ta amince su dinga bada irin wannan shahada.

 

a cewar sanarwar kasar nan na da jami’o’i 162 wadanda 41 mallakar gwamnatin tarayya ne inda 47 suka zama mallakar jihohi sai kuma guda 74 da suka zama masu zaman kan su

 

Sanarwar ta ce cikin jami’o’i 41 na gwamnatin tarayya hukumar ta amince da guda 26 ne kawai su dinga bada shahadar, da suka hadar da jami’ar Bayero da ke nan Kano da kuma Ahmadu Bello dake Zaria, da kuma jami’ar Usmanu dan fodiyo da ke Sokoto.

 

Haka kuma cikin jami’o’i mallakar jihohi, 25 ne kawai aka amince da su bada wannan shahada da suka hadar jami’ar kimiyya da fasha da ke garin Wudil da kuma jami’ar Umaru Musa yar Aduwa da ke jihar Katsina.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!