Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Gwamnatin jihar Kaduna ta kori sabbin ma’aikatan ta kimanin 5000

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta kori sabbin ma’aikatan ta kimanin 5000 da dauka aiki domin maye gurbin malaman firamare sama da 20 da ta kora a baya makwanni kadan bayan da suka takardar kama aiki.

Kwamishinan ilimi na jihar ta Kaduna Alhaji Ja’afaru Sani shi ne ya bayyana haka da yammacin jiya, inda ya ce an kori sabbin malaman ne sakamakon cewar suna cikin wadanda aka kora a baya kuma sun bi ta barauniyar hanya ne suka sake tsintar kan su a cikin ma’aikatan.

A baya dai jihar ta Kaduna ta kori malaman firamare dubu 22 wadanda suka kasa cin jarrabawar gwaji ta yan aji hudu na firamare da aka yi musu ta kuma sanar da maye gurbin su da wasu sabbin malaman da ta sake dauka

Ka zalika gwamnatin ta dauki matakin korar ne bayan da aka baiwa sabbin ma’aikatan takardar kama aiki amma suka gaza rubuta wasikar amincewa da karbar aiki, lamarin da ya sanya gwamnatin sake gudanar da wata jarrabawar gwajin akan sabbin ma’aikatan.

A cewar kwamishinan a karshen tantancewar gwamnatin ta gano wasu dubu hudu da dari biyar da 62 da ba su cancanta ba inda ta ce sun shigo cikin shirin ne ta barauniyar hanya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!