Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Gwamnatin Kaduna ta mayar da Malaman firamare fiye da 1,000 da ta sallama bakin aiki

Published

on

Gwamnatin jihar  Kaduna ta amince da mayar da malaman makarantar firamare 1244 da ta sallama bakin aiki.

Mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna Hajiya Hauwa Muhammad ce ta bayyana hakan, cikin sanarwar da aka fitar a jiya Laraba.

Hajiya Hauwa ta ce malamai 1,266 ne aka yi wa jarrabawar gwajin cancantar, yayin da 22 a cikinsu aka tsame su daga jadawalin albashin gwamnati.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa a Yunin 2022 ne, ma’aikatar ilimin ta kori malaman Firamare 2,357 saboda gaza tsallake jarrabawar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!