Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da dokar ta-baci a fannin ilimi

Published

on

Mai kishi da jajircewa wajen ganin an ceto fannin ilimi daga durkushewa gaba daya, Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf a yau ya ayyana dokar ta-baci akan ilimi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya rabawa manema labarai a

Da yake gabatar da jawabinsa a wani gagarumin taron da aka gudanar a gidan gwamnati, Gwamna Abba Kabir ya ce, ayyana dokar ta-baci zai baiwa gwamnati damar daukar kwakkwaran matakai don magance matsalolin da suka addabi fannin a fadin jihar.

Ya kara da cewa sanarwar za ta baiwa gwamnati damar tattara kayan aiki, da aiwatar da gyare-gyare cikin gaggawa, da kuma mai da hankali kan dabarun da za su sake gina hanyoyin ilimi, samar da kayayyakin da suka dace, matakin da zai share fagen samar da inganci ga kowane yaro a jihar Kano.

Alhaji Abba Kabir ya bayyana tanade-tanaden da aka yi don karfafa harkar ilimi shiyasa aka ware 29.95% na kasafin kudin 2024; domin kula da ɓangaren ilimi.

Haka kuma gwamnan Ya bayyana shirin gina karin dakunan gwaje-gwaje 300, da shirin gina ajujuwa 1000 a cikin makarantun jihar da kuma bude dukkan makarantun kwana da gwamnatin da ta shude ta rufe.

Sauran su ne; shirin sake gyara dukkan makarantun firamare da kananan sakandare, azuzuwan 28,264 a cikin shekaru uku masu zuwa don samarwa da yara ilimi mai inganci da kuma bayar da abinci ga kowane yaro a kowace rana a dukkan makarantun firamare tare da dawo da rarraba kayan sawa kyauta ga duk daliban firamare I da dai sauransu.

Hakazalika, gwamnatin jihar ta bayar da aikin ga malamai 5,632 na BESDA (Better Education Service Delivery for All) da aka amince da daukar karin malamai 10,000.

Gwamnatin ta kuma amince da bayar da rancen kudi naira miliyan 300 ga malaman da ke aiki a karkashin hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar (SUBEB) a fadin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!