Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ragin kudin hayar da muka samu na gidan haya zai rage farashin kayayyaki a kasuwar kantin kwari

Published

on

Yan kasuwar a kasuwar kantin kwari sun ce mutane za su samu saukin kayan suturun kasuwar  a wannan lokacin da ake ciki na tsadar kayyayaki sakamakon ragin kudin hayar shaguna da suka samu a kasuwar.

Shugaban kungiyar Mumfarka Traders dake kasuwar kantin kwari Alhaji Yusuf M Yusuf, ya bayyana haka yayin da ya jagoranci yan kasuwar da ke haya a shagunan gidan Alaramma wajan karrama shugaban dake kula da gidaje da kadarorin alaramma.

Alhaji Yusuf M Yusuf ya kara da cewa abun a yaba ne kuma a yi koyi  yadda masu wannan gida suka yiwa yan kasuwa  ragi duba da yanayin da yan kasuwa suke ciki kuma wannan saukin zai shafi masu sayen kaya a kasuwar.

Ya kara da cewa akwai shagunan da suka sami ragin kimanin naira dubu dari da hamsin wasu kuma dubu dari wasu shagunan kuma dubu hamsin

Daya yake jawabi bayan karbar lambar yabon da kungiyar yan kasuwar suka kawo masa shugaban rukunin gidaje da kadarorin gidan Alhaji Musa Haruna Alaramma yayi kira ga sauran masu gidaje da su duba yanayin da ake ciki domin saukakawa yan kasuwar.

Ya kuma yabawa hadin kan mazauna gidan musamman yadda suke baiwa shugabannin su hadin kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!