Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin jihar Kano ta nada sabon Kwamishinan ayyuka.

Published

on

Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya rantsar da Injiniya Idris wada Saleh a matsayin sabon Kwamishina a ranar Laraba .

Babbar lauyar gwamnati Amina Ƴar Gaya ce ta rantsar dashi a madadin gwamnan yayin taron majalisar zartarwa.

Gwamna Ganduje ya ce “Mun tura sabon kwamishinan zuwa ma’aikatar ayyuka domin ya ci gaba da gudanar da ayyukan ta”

“Mun kuma aike da tsohon kwamishinan ayyuka Idris Garba unguwar Rimi zuwa ma’aikatar kimiyya da fasaha ta Kano don ya ci gaba da aiki a can”.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kuma buƙaci sabon kwamishinan ayyukan ya gudanar da aikin sa yadda zai ciyar da Kano gaba.

Idan ba a manta ba dai, sabon kwamishinan ayyuka Injiniya Idris Wada Saleh shi ne ya ke riƙe muƙamin shugaban hukumar kula da gyaran titunan Kano gabanin naɗa shi a matsayin Kwamishina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!