Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

Kasafin 2022: Gwamna Badaru ya gabatar da Naira biliyan 177 ga majalisar dokoki

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2022.

Kasafin dai ya kai Naira biliyan 177 da miliyan 179.

Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ne ya gabatar da kasafin a gaban zauran majalisar dokokin Jihar.

Gwamna Badaru yace, an warewa ɓangaren manyan ayyuka Naira biliyan 91, yayin da ɓangaren ayyukan yau da kullum aka ware masa Naira biliyan 83.

A kasafin kuɗin ɓangaren ilimi ya samu kaso mafi tsoka da ya kai Naira biliyan 32.

Gwamnan ya ƙara da cewa wannan shi ne kasafin gwamnatinsa na farko da ɓangaren ayyuka yafi samun kaso mai yawa.

Shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Idris Garba Jahun ya bai wa gwamnan tabbacin kammala aikin kasafin kafin watan Janairun 2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!