ilimi
Da ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Kano ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu
Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu.
Kwamishinan ilimi Malam Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ne ya bayyana hakan da yammacin ranar Litinin.
“Na soke duk wani lasisi na mallakar makarantu masu zaman kan su a Kano daga yanzu mun soke su, har sai mun ɗauki matakin tantance su”.
“Za mu kafa kwamiti mai ƙarfi da zai tantance makarantun domin gwamnatin jihar Kano na da tsari, idan kwamitin ya kammala aikin sa za mu tantance waɗanda za su ci gaba da aiki a Kano bisa cancanta da kuma waɗanda za mu dakatar har abada” a cewa Ƙiru.
Malam Sanusi ya kuma ce, gwamnatin Kano ta lura da yadda wasu mutane suka mayar da buɗe makarantu masu zaman kan su tamkar kasuwanni wanda kuma hakan ya saba doka.
Wannan dai na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da aka gano shugaban makarantar Nobel Kids Academy da laifin yin garkuwa da ɗalibar nan Hanifa wadda aka sace tsawon wata guda tare da kashe ta.
You must be logged in to post a comment Login