Labarai
Gwamnatin jihar Kano za ta fara biyan ma’aikata 9,332 da aka tantance a watan nan
Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta kammala tantance ma’aikatan da tsohuwar gwamnati ta ɗauka su 12,566 inda adadin wa’inda suka cancanta su 9,332 ne adan haka gwamnatin ta bada umarci a dawo da su kan tsarin biyan albashi cikin wannan wata
Sakataren gwamnatin jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ne yayi wannan jawabin yayin da yake ganawa da manema labarai a safiyar yau juma’a 24 ga watan Nuwamba domin tabbatar da an dawo da wa’inda suka cika ƙaƙida tsarin biyan albashi a wani ɓangare na samar da ci gaba ga jihar Kano
Haka kuma gwamnatin Kano ta ce a baya an ɗauki ma’aikatan ne ba tare da an tanadi kuɗin da za’a biya su albashi ba, kasancewar indai gwamnati zata dauki ma’aikata to akan sanya su a cikin kasafi na ƙarshen shekara, amma wa’innan ma’aikatan an basu aiki kuma babu su a cikin kasafin shekarar da ta gabata
Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ya ce cikin wa’inda aka tantance an sami masu takardun bogi
kuma a yayin daukar aikin an tura wasu guraren da basu da gogewa akai, adan hakan yanzu haka za’a tura duk wa’inda aka tantance inda ya da ce da abin da mutun ya karanta
Haka kuma Baffa Bichi ya ce bincike ya gano cewa an ɗauki dalibai da suke a matsayin firamare da sakandare an sanya su a tsarin biyan albashi
Gwamnatin jihar Kano kuma ta bayar da umarnin a tantance wa’inda suke da takardun aiki ba’a biyan su domin tabbatar da su a matsayin ma’aikata
You must be logged in to post a comment Login