Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamnatin Jihar Kano zata mayar da kasuwar magani zuwa Dangwauro

Published

on

 

Kwamitin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na jihar Kano ya kwace katan 147 na jabun magunguna da aka ajiye su a wani kango dake unguwar Dabai a karamar hukumar Dala.

Lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan kammala tattare magungunan Darktan kula da bangaran magunguna na hukumar kula da Asibitoci ta jihar Kano Ghali Sule ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Jabun Magunguna

Ghali Sule yace an samu nasarar cafke jabun magungunan ne sakamakon bayanan sirri da wani dan kishin kasa ya kaiwa hukumar musamman ma kai kawo da wasu mutane da ba’a san ko su waye ba suka rika yi a yankin.

Kano : An kama magungunan da aka haramta na naira biliyan 5

Ghali Sule yace a yanzu shirye shirye sun yi nisa domin dauke kasuwar magunguna ta Sabongari zuwa matsugunin ta na din din din dake garin Dangwauro a karamar hukumar Kumbotso.

Pharmacist Ghali Sule ya kuma bukaci al’umma da su taimakawa gwamnati wajen yaki da sha da fatauci da miyagun kwayoyi..

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!