Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

An fara aikin tsaftace makabartu a Kano

Published

on

Wasu al’umma a jihar Kano sun fara wani yunkuri na musamman domin gyaran makabartun dake jihar.

A jiya Alhamis ne aka fara aikin gyara da tsaftace makabartun inda aka fara da makabartar Tarauni dake birnin Kano, wata mai kishin al’umma mai suna Hajiya Zainab Ahmad ce ta jagoranci aikin, ta kuma bayyanawa Freedom Radio cewa aikin na tafiya yadda ya kamata sannan akwai bukatar karin fitowar jama’a domin bada gudummuwarsu da karfinsu wajen dorewar aikin.

Al’umma daban-daban da kungiyoyi da dama ne suka samu halartar aikin a jiya Alhamis.

Kalli hotunan yadda aikin ya gudana:

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!