Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe wurin haƙar ma’adanai

Published

on

Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe wurin haƙar ma’adanai na Zuzungi Kataeregi da ke Karamar Hukumar Katcha na wucin gadi bayan wani rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’in tsaro.

Wannan na cikin sanarwar da Babban Sakataren Ma’aikatar Albarkatun Ma’adanai ta Jihar, Idris Legbo, ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta bayyana cewa rikicin ya janyo lalata motar sintiri ta hadin gwiwa, lamarin da Gwamnati ta bayyana a matsayin kalubalantar ikon gwamnati da kuma halattaccen aikin hakar ma’adanai.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya taso ne sakamakon takaddama tsakanin masu safarar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da jami’an tsaro da ke aiki a wurin.

Gwamnatin ta jaddada cewa wurin na da cikakkiyar lasisi kuma yana bin dukkan tanade-tanaden doka, tare da alkawarin daukar matakan da suka dace domin dawo da zaman lafiya a yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!