Labarai
Gwamnatin Kaduna da Bankin musulunci sun gina makarantun sakandiren kimiyya da fasaha 6
Gwamnatin jihar Kaduna tare da hadin gwiwar Bankin musulunci sun gina makarantun sakandiren kimiyya da fasaha guda shida kan kudi sama da naira biliyan dari bakwai da sittin da daya, domin inganta bangaren kimiyya da fasaha a jihar.
Kwamishinan ilimi na jihar Ja’afaru Sani ne ya bayyana haka, yayin wani rangadi da ya kai makarantun.
Kwamishinan ilimin ya ce kowacce mazabar Sanata, za’a gina makarantun sakandiren kimiyyar da fasaha biyu, wadanda kuma za’a wadata su da kayayyakin koyo da koyarwa na zamani, wanda zai yi daidai da tsarin horas da kimiyya da fasaha.
Ya kara da cewa makarantun ana gina su a yankunan Manchok da Jere da Buruku da Rigachukun da Pambeguwa da kuma Hunkuyi.
Sai dai yace ginin da ake yi a Manchok da Buruku da Kuma Rigachukun bai yi nisa kamar wadda ake yi a Jere ba, amma yan kwangilar da ke ginin wuraren sun ce za suyi kokarin kammalawa a kan lokaci.