Connect with us

Labarai

Rundunar yan sandan kasar nan ta yi nasarar samo sandar majalisar dattijai

Published

on

Rundunar yan sandan kasar nan ta yi nasarar samo sandar majalisar dattijai da wasu bata gari suka dauke ana tsaka da zaman majalisar na jiya Laraba.

Ana dai zargin wasu gungun yan daba ne suka yi awon gaba da sandar a dai-dai lokacin da ake zaman majalisar a jiya.

Al’amarin da ya sanya zauran majalisar ya bada umarnin gaggawa ga babban sifeton yan sandan kasar nan Ibrahim Idris da kuma Darakta Janar na hukumar tsaron sirri ta DSS Lawan Daura da su tabbatar an dawo da sandar a cikin abinda bai gaza awanni 24 ba.

Cikin wata sanarwa da rundunar yan sandan ta fitar da sanyin safiyar yau Alhamis ta bakin mataimakin jami’in yada labaran ta SP Aremu Adeniran ta ce wadanda ake zargin da sace sandar, sun yar da ita ne a karkashin gada, kafin isa Kofar birni da ke hanyar zuwa filin jirgin saman Abuja.

Adeniran ya ce haka zalika babban sifeton yan sandan kasar nan ya umarci Kwamishinan yan sandan birnin tarayya Abuja da ya kara tsananta  tsaro a harabar majalisar dattijan

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!