Connect with us

Labarai

Jami’an tsaro sun cafke Sanata Dino Melaye a filin Jirgin saman Abuja

Published

on

Jami’an tsaro sun cafke dan majalisar Dattijai mai wakiltar Kogi ta yamma Sanata Dino Melaye, a filin  Jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayya Abuja.

Sanata Dino Melaye ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter inda ya ce yana kan hanyarsa ta tafiya kasar Morocco ne domin ziyarar aiki sai jami’an tsaro suka kama shi, sannan daga bisani suka mika shi hannun ‘yan-sanda.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar shige-da-fice ta kasa ne suka kama Sanata Dino Melaye.

A baya dai Rundunar ‘yan-sandan kasar nan ta ayyana Dino Melaye a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo bisa zarginsa da hannu kan kisa tare kuma da mara baya ga wasu tsageru masu rike da makami.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!