Labarai
Gwamnatin Kano ta nemi hadin kan kungiyoyin aikin gayya

Gwamnatin Kano ta ce ta nemi hadin kan kungiyoyin aikin gayya wajan ya she maguda nan ruwa tare da kwashe dagwalo a fadin jihar.
Kwamishinan Muhalli na jihar Dakta Dahiru Muhd Hashim ne ya bayyana hakan ,ya ce tuni shirye shirye sunyi nisa na fara aikin.
Ya kara da cewa nan gaba kadan za’a kaddamar da shirin kwashe magudanan ruwan dake manyan tituna da ungwannin dake jihar nan.
kwamishinan ya yi kira ga al’umma da su dena zuba shara a magudanan ruwa yana mai cewa gwamnati za ta hukunta duk wanda ta samu da laifi.
You must be logged in to post a comment Login