Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta ɗage aikin tsaftar Muhalli

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta dakatar da aikin duben tsaftar muhalli na watan nan da muke ciki na Afrilu domin bai wa daliban da za su rubuta jarrabawar shiga makarantun gaba da Sakandare ta JAMB damar isa cibiyoyin jarrabawar a kan lokaci.

Kwamishinan muhalli da kula da sauyin yanayi Dakta Dahir Muhammad Hashim, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwar da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Isma’il Garba Gwammaja ya fitar yau Alhamis.

Kwamishinan ta cikin sanarwar ya kuma bayyana cewa, dakatarwar ta wucin gadi ce watau ta iya wannan watan kaɗai, kuma za a ci gaba da aikin tsaftar mahalli a wata mai kamawa na Mayu.

Haka kuma, ya yi kira ga mazauna Kano da su bai wa hukuma hadin kai da fahimtar dalilin da ya sa aka yanke wannan hukunci musamman na ganin cewa ayyukan tsaftar muhalli ba su ci karo da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a jihar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!