Labaran Kano
Gwamnatin Kano ta amince da biyan Albashin Maris gabanin Sallah

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da biyan albashin watan Maris na shekarar 2026 da wuri ga dukkan ma’aikatan gwamnati a jihar, domin ba su damar yin shirye-shiryen bukukuwan karamar Sallah cikin sauki.
Mukaddashiyar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a gaggauta sakin kudaden albashin domin ma’aikata su samu damar gudanar da bukukuwan Eid-el-Fitr cikin walwala.
Ta kuma ce matakin biyan albashin da wuri yana nuna yadda gwamnati ke kula da jin dadin ma’aikata da kuma yaba gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban jihar, tare da yin kira gare su da su ci gaba da nuna jajircewa da kwarewa wajen gudanar da ayyukansu.
You must be logged in to post a comment Login