Labarai
Gwamnatin za ta kashe Naira biliyan 4 a wasu ayyuka
Gwamnatin Jihar Kano ta ce, za ta kashe kuɗin da za ta gudanar da wasu ayyuka kudi sama da Biliyan 4 da miliyan 882 da dubu 378 domin yin wasu aikace-aikace a faɗin jihar Kano.
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a daren jiya ta bakin Kwamishinan yaɗa labarai Baba Halilu Ɗantiye jim kaɗan bayan kammala zaman zartarwa da gwamnatin ta saba yi a duk sati domin tattaunawa akan abin da ya shafi gwamnati.
Baba Halilu Ɗantiye ya kuma ce ‘wannan Kuɗaɗe da aka fitar da’ayi aiki ne da su a bangarori da dama na ma’aikatun gwamnati’.
Ka zalika gwamnatin ta ce ta ware sama da Biliyan 3 da zata kai ɗalibai ƙasashen waje a cewar Kwamishinan harkokin ilimi mai zurfi Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata.
Freedom Radio ra ruwaito cewa, Gwamnatin ta kaddamar da kwamitin da zai jagorancin rabon kayan tallafin abinci ƙarƙashin jagorancin sakataren Dakta Abdullahi Baffa Bichi da zai fara aiki a yau domin bayar da tallafin ga al’umma.
Rahoton:Umar Abdullahi Sheka
You must be logged in to post a comment Login