Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NAHCON ta karbi sabon jadawali daga Saudi Arebiya

Published

on

Hukumar kula da aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON tace hukumomin kula da aikin Hajji da Umrah na kasar Saudi Arebiya sun baiwa hukumar tsarin jadawalin yadda za’a gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024 mai zuwa domin ganin an kammala komai akan lokaci.

Shugaban hukumar Zikirullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan, lokacin da yake zantawa da menama labarai dan gane da irin yadda hukumar ta sami nasarar kammala ibadar aikin Hajjin daya gabata.

Zikirullah Kunle Hassan wanda kwamishinan kula da ma’aikata da harkokin kudi na hukumar Nura Hassan Yakai yayi jawani cikin harshen Hausa amadadinsa, yace kawo yanzu duk wasu tsare – tsare na yadda aikin Hajjin shekara mai zuwa zai gudana hukumar kula da aikin Hajji ta kasar Saudi Arebiya ta mika komai ga hukumar tasu.

Ya ce ‘hakan yasa sukayi taro da shuwagabannin hukumomin kula da jin dadin alhazai na jihohin kasar nan akan lamarin’.

Haka zalika Alhaji Nura Hassan Yakasai yayi karin bayani akan hanyoyin da suke bi wajen warware matsalar wadanda suka biya kudinsu da niyyar zasuyi aikin Hajji amma wata LaLalura ta hanasu ko Kuma mutuwa.

Freedom Radio ta rawaiti cewa nan da kwanaki kadan hukumar zata fara duk Wani shirye-shiryen aikin hajjin shekarar 2024 domin ganin anyi komai cikin nasara.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!