Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta bawa mazauna Tal’udu da Sani Mainagge wa’adin tashi domin fara aikin Gada bayan biyan su haƙƙokin su.

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bai wa al’ummar Unguwannin Tal’udu da Sani Mainagge da Kabuga waɗanda aikin Gadar Sama ya shafi gidajensu wa’adin fara kwashe kayansu domin fara aiki.

 

Daraktan harkokin kuɗi da mulki na ma’aikatar kasa daya wakilci kwamishan, Alhaji Hamid Sidi Ali ya ce a yanzu haka gwamnatin Kano ta biya diyyar gidajen da aikin gadar ya shafa dan haka gwamati take kira ga masu gidajen dasu fara haɗa kayayyakinsu kafin fara wannan aiki.

 

Muhammad Yahuzu babban sakatare a ma’aikatar kasa ya ce Gwamnatin Kano ta samar da matakan tsaro domin fara wannan aiki .

 

Shugaban kungiyar wadanda aikin ya shafa Alhaji Abba Aminu Imam ya godewa Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf bisa cika alkawari da yayi na basu diyya mai kyau ta gidajensu tare da basu filotai a wasu mahimman wurare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!