Labarai
Gwamnatin Kano ta bukaci rundunar ‘Yan-sanda da su gaggauta sakin Muhuyi Magaji Rimin Gadon

Ma’aikatar Shari’a ta jihar Kano zargi jami’an yan sanda da kama tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Barriester Muhyi Magaji Rimin Gado.
Kwamishinan Shari’a na Kano Barriester Abdulkarim Kabiru Maude SAN ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai.
Ya kuma bukaci rundunar yan sandan da suka kamashi da su gaggauta sakin sa, duba da acewar sa ba abi ta hanyar da ta daceba wajen kamen da akai masa ba.
Barriester Abdulkarim Kabiru Maude SAN ya kuma zargi wasu daga cikin mutane dakeyin amfani da gwamnatin tarayya wajen cusgunawa jami’an gwamnatin Kano.
Rahotonni na cewar yanzu haka Jami’an tsaro na tsare da Muhyi a birnin Tarayya Abuja.
You must be logged in to post a comment Login