Labarai
Gwamnatin Kano ta ce tana goyon bayan shirin AGILE
Gwamnatin jihar kano ta ce zata ci gaba goyon bayan shirin tallafawa yara mata na AGILE, domin tsari ne da zai samarwa da yara mata hanyar karatu musamman yaran da suke a yankin karkara da kuma gina makarantu da gyaran su.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar kano Baba Halilu Ɗan Tiye ne ya bayyana hakan yau 05 ga watan Janairun 2024 yayin wata ziyara da shugabannin shirin suka kawo masa domin ƙara sanar da gwamnati yadda tsarin na AGILE yake da kuma irin abin da tsarin yake son tabbatarwa.
Haka kuma kwamishinan ya ce gwamnati a shirye take wajen ganin ta bayar da goyon bayan ta ga wannan tsarin domin abu ne da zai ƙara inganta harkar ilimi a faɗin jihar kano.
Da yake jawabi mataimakin shugaban shirin reshen kano Alhaji Salisu Idris ya ce wannan tsarin na AGILE tsari ne da yake shiga lungu da saƙo na jihar nan domin tallafawa yara mata a ɓangaren ilimi da kuma gina makarantu da kuma wayar wa da mata kai kan yadda zasu gudanar da rayuwar su ta yau da kullum.
Gwamnatin jihar kano ta ce zata ci gaba da goyon bayan tsarin musamman yadda a yanzu shine yake shiga yankunan karkara suna gina makarantu
You must be logged in to post a comment Login