Addini
Gwamnatin Kano ta ce zata ɗauki matakin Shari’a kan zargin Malam Lawan Triumph na ɓatanci a cikin wani karatu da yayi.

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ɗauki mataki dai-dai da abin da shari’a ta tanadar kan zargin da ake yi wa Malam Lawan Triumph na ɓatanci a cikin wani karatu da yayi.
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin wata zanga-zangar lumana da matasa suka gudanar tare da kawo ƙorafi a fadar gidan gwamnatin Kano.
A cewar gwamnan Abba kabir Yusuf gwamnati ba zata yi watsi da kowanne irin zargi da al’umma suka gabatar ba, musamman idan ya shafi cin mutunci ko rashin mutunta ɗabi’un addini da al’ada, inda Ya ce gwamnati zata tabbatar da adalci ta hanyar bin dokoki da ka’idojin da suka dace.
Da suke jawabi Matasan da suka gudanar da zanga-zangar da suka fito daga sassa daban-daban na Kano sun nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira kalaman batanci na Malam Lawan Triumph, inda Suka roƙi gwamnati ta dauki matakin da zai zama darasi ga kowa wajen kaucewa kalaman da ka iya tunzura jama’a.
You must be logged in to post a comment Login