Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta ci gaba yin rusau a Massallacin Idi

Published

on

A daren jiya ne Gwamnatin jihar Kano ta ci gaba da rushe gine-ginen da ke cikin filin Masallacin Idi na Ƙofar Mata.

Motocin Rusau huɗu ne suka ci gaba da rushe gine-ginen Shaguna ɗari da aka yi a cikin filin idin.

Da ya ke yin ƙarin bayani a kai, shugaban hukumar tsara birane ta Kano Arch. Ibrahim Yakubu ya shaida wa Freedom Radio cewa abin takaici ne ace an gine filin Babban Masallacin Idi na garin da ke alfahari da Musulunci.

Ya kuma yi kira ga waɗanda ke da kayayyaki a wuraren da aka sanya wa jan fenti da su gaggauta kwashewa domin ci gaba da wannan rushe-rushen ya zama dole ba gudu ba ja da baya a cewarsa.

Wanda ya ce ‘ba gudu, ba ja da baya, sai gwamnatin ta tabbatar ta dawo da Kano dai-dai da tsarin da aka zanata a kai’.

Rahoton: Bashir Sharfadi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!