Labarai
Gwamnatin Kano ta cimma mastaya da Ƴan Adaidaita
Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Hukumar kula da zurga-zurgar ababen hawa KAROTA ta cimma matsaya da matuƙa baburan adaidaita sahu waɗanda suka tafi yajin aiki a makon da ya gabata, domin nuna ƙin amincewar su akan kuɗin da Gwamnati saka musu sabunta izinin tuƙi.
A zaman da aka yi a ranar Laraba a ofishin Ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Kano da ke Farm Center, an shafe sama da sa’o’i hudu ana tattaunawa tsakanin lauyan ƴan adaidaitan Abba Hikima Fagge da kuma shugaban hukumar KAROTA Dakta Baffa Babba Ɗan Agundi dake wakiltar Gwamnati, da wasu cikin ƴan adaidaitan, an amince da rage kuɗin sabunta izinin tuƙin adaidaitar daga Naira 8000 zuwa 5000.
Zaman ya kuma amince da biyan harajin kulum-kullum har da ranar Lahadi, sannan an amince kowane ɗan adaidaita sahu ya biya wannan kuɗi nan da ƙarshen watan biyu na Febreru na wannan shekarar.
A zantawar lauyan matuƙa baburan adaidaitan Abba Hikima da Freedom Radio, ya yi kira ga matuƙan da su sabunta izinin tuƙin cikin lokacin da aka saka, domin kaucewa biyan tsohon kuɗin da gwamnati ta saka.
You must be logged in to post a comment Login