Connect with us

Labarai

Zamu fara kama motocin gidan gwamnati muddin suka gaza biyan kudin haraji -KAROTA

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano  KAROTA ta bukaci gwamnatin jihar Kano da sauran jam’iyyun siyasa  dasu fara kokarin biyan kudin hajarin lika hotunan ‘yan siyasa na jikin motocin da ake sanya wa

Baffa Babba Dangundi ya bayyana hakan ne, lokacin da yake karbar bakuncin wasu kungiyoyin direbobin Adaidaita sahu da suka kawo masa ziyara domin nuna goyan bayansu da sabon tsarin yin rijasta domin tsaftace harkar sana’ar tuka adaidaita Sahu a Kano.

Haka zalika,Baffa Babba Danagundi ya kara da cewa matukar aka shiga sabuwar shekara kuma majalisar jihar Kano suka amince da kafa dokar shakka babu duk wanda ya lika kowane irin hoto a babur dinsa wajibi ne ya biya kudin haraji a hukumar KAROTA.

Mun fara aiki kan masu Keke da babura -KAROTA

An cafke direban da ake zargin yayi sanadin mutuwar jami’in KAROTA

Hukumar KAROTA ta nemi a kebe mata Naira biliyan guda

Wakilin mu  Abdulkarim Muhammd Abdulkarim Tukuntawa ya rawaito cewa, Shugaban Hukumar ta Karota Baffa Babba yace baza su saurarawa duk wanda bai yi sabuwar rijistar ba, za su dauki mataki mai tsauri akan duk wanda ya gaza yin rijistar.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!