Labarai
Gwamnatin Kano ta fara zawarci masu zuba jari a bangarorin samar da wutar lantarki
Gwamnatin jihar Kano ta fara zawarcin masu zuba jari a bangarorin samar da wutar lantarki da aikin gona da samar da ayyukan more rayuwa domin bunkasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka, yana mai cewa, tuni suka fara tattaunawa da wasu masu sha’awar zuba jari a jihar.
Ya ce gwamnatin Kano ta yi alkawari wa masu samar musu da filaye da rage musu haraji da samar musu da tsaro da kuma kayayyakin more rayuwa.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taron duniya da ake gudanarwa shekara-shekara karo na takwas kan zuba jari a birnin Dubai na hadaddiyar Daular Larabawa.
Cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na gidan gwamnatin Kano Aminu Yassar ya fitar, ta ce, gwamna Ganduje ya bukaci ‘yan kasuwa na kasa da kasa da su yi amfani da damar da gwamnatin Kano ta ba su domin zuba jari a jihar.