Labaran Kano
Gwamnatin Kano ta gaggauta kafa hukumar masu bukata ta musamman – KCSF
Gamayyar kungiyoyin fararan hula a jihar Kano KCSF ta bukaci gwamnatin jihar da ta hanzarta kafa hukumar dake kula da mutane masu bukata ta musamman kamar yadda ta alkawarta.
A cewar ta kafa hukumar na da matukar muhimmanci da zai samar da hadinkai da kuma jindadi da walwalar mutanen dake da nakasa.
Hakan na zuwa ne yayin taron shekara da kungiyar ta gabatar a ranar 1 ga watan Janairun 2025, karkashin jagorancin shugabanta Kwamred Muhammad Bello.
A cewar shugaban kungiyar jinkirin kafa hukumar yana a matsayin karya dokar masu bukata ta musamman ta Najeriya da akai a shekarar 2019.
Haka zalika ya ce har yanzu mutanan dake da bukata ta musamman suna karancin samun guraben aiki masu muhimmanci a hukumomin gwamnati “wanda samar da hukumar zai magance matsalar”.
Haka zalika kungiyar ta bukaci majalisar dokokin jihar Kano, da Sarakuna, da Shugabannin Addinai, da Kungiyoyi na masu zaman kansu da su bayar da goyan baya wajen ganin gwamnati ta samar da hukumar ta masu bukata ta musamman, da kuma hana yadda ake mayar da su koma baya a harkoki da dama.
You must be logged in to post a comment Login