Connect with us

Labarai

Karrama ni tamkar kalubale ne -Abdullateef Jos

Published

on

Manajan labarai na nan tashar Freedom Radio Malam Abdullateef Abubakar Jos, ya bukaci ‘yan jarida da sauran al’umma da su kara zage dantse wajen gudanar da ayyukansu tsakani da Allah.

Malam Abdullateef Abubakar Jos, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da ya karbi shaidar karramawa da kungiyar masu bukata ta musamman ta ba shi.

Da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kyautar, ya bayyana cewa ya dauki kyautar a matsayin kalubalen da zai kara zaburar da shi wajen kara kaimi a gudanar da aikinsa.

Kungiyar dai ta raba kyaututtuka da lambar girmamawa ne yayin taron bikin ranar masu bukata ta musamman da ake gudanarwa a kowacce ranar 3 ga watan Disambar kowacce shekara.

A yayin taron dai kungiyar ta karrama mutane da dama da suka hadar da Hajiya Halima Shekarau da kwamishinan lafiya na jihar Kano da shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na kasa kwamared Ibrahim Khalil da sauran mutane da dama.

Da yake jawabi yayin taron shugaban karamar hukumar Nassarawa kuma shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Kano Lamin Sani Kawaji, wanda ya kasance mai masaukin baki a taron, ya bayyana cewa zai yi dukkan mai yiwuwa wajen bibiyar gwamnatin don ganin tana aiwatar da dokar masu bukata ta musamman da ta kafa tun a baya.

A nata jawabin, shugabar kungiyar masu bukata ta musamman  shiyyar arewa maso yamma  Bilkisu Ado Zango, ta ce akwai bukatar gwamnati ta samar musu da wasu mukamai a gwamnatance wanda hakan ne zai tabbatar musu da cewa gwamnatin tana tafiya da su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,149 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!