Labarai
Gwamnatin Kano ta gargaɗi yan kwangilar da ke jan Kafa

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ‘yan kwangilar da ke jan kafa wajen gudanar da ayyukan da ta basu, kan su tabbatar sun kammala a kan lokaci.
Kwamishinan kula da bibiyar aiyyukan gwamnati Kwamred Nura Iro Ma’aji Sumaila, ne ya yi wannan gargadin yayin ziyarar duba aiyyukan kwangilar da ake yi a wasu wurare 9.
Daga cikin wuraren da kwamishinan ya ziyarta yayin duba aikin, sun hada da Titin Gadar sama da ta kasa da ke Dan-Agundi sai aikin gadar Tal’udu , inda kwamishinan ya ce ana bukatar kammala aikin a kan lokaci.
Kwamred Nura Iro Ma’aji Sumaila, ya kuma bayyana farin cikinsa dangane da aikin da ake gudanarwa a Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil , inda nan ma ya bukaci a kammala shi cikin kasa da mako guda.
Yayin ziyarar dai, kwamishinan ya duba ayyukan da ake gudanarwa a Asibitin Nuhu Bamalli da ma’aikatar yawon bude idanu da Al’adu da cibiyar Musulunci da ke filin Idi na Kofar Mata.
You must be logged in to post a comment Login