ilimi
Dalibai sun bai wa hukumar lura da lamunin Ilimi wa’adi kwanaki 5

Kungiyar daliban Kwalejojin kimiyya da fasaha watau Polytechnic na Najeriya sun bai wa hukumar da ke lura da bayar da lamunin Ilimi wa’adin kwanaki biyar kan ta yi cikakken bayanin yadda aka kashe kudaden daliban.
Hakan dai na zuwa ne bayan da wasu zarge-zarge suka janyo ce-ce-ku-ce, inda har ta kai ga wata zanga-zangar da mambobin kungiyar dalibai suka gudanar a ranar Litinin da ta gabata.
Yayin zanga-zangar da daliban sun tare babbar hanyar Lagos zuwa birnin Ibadan.
Duk wanann na zuwa ne biyo bayan zargin da hukumar wayar da kan jama’a ta kasa ta yi na cewa wasu cibiyoyi tare da hadin gwiwar bankuna na ci gaba da cire kudaden rancen dalibai na bogi.
You must be logged in to post a comment Login