Labarai
Gwamnatin Kano ta haramta lika hotuna Fastoci a jikin Gine-gine

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata fara hukunta masu lika fasta wato duk wata takarda da take dauke sako a gine-ginen gwamnati.
A wata sanarwa da ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta fitar, ta bayyana damuwarta kan yadda ake bata ababen more rayuwa na jama’a, musamman shataletalen hanyoyi, tsakiyar tituna, gefen hanyoyi, gadar sama da sauran wuraren da aka kawata a cikin birnin.
Ma’aikatar ta ce wannan dabi’a na rage kokarin da gwamnati ke yi na kawata birni da farfaɗo da muhalli, tare da haddasa gurbacewar yanayi, lalacewar kayayyakin more rayuwa da kuma rage ganin hanya a manyan tituna.
You must be logged in to post a comment Login