Labarai
Gwamnatin Kano ta kaddamar da shirin bunkasa harkokin Noma

Gwamnatin jihar Kano, ta kaddamar da sabon shirin bunkasa harkokin noman rani da na damuna ta hanyar bai wa manoman da za su ci gajiyar shirin horo a kan yadda za su sarrafa sabbin Injinan aikin Noman zamani domin su rika amfani da su kamar yadda sauran kasashen duniya da suka ci gaba suke yi.
Kwamishinan ma’aikatar raya Karkara da ci gaban al’umma, Abdulkadir Abdussalam, ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci bai wa matasa 200 horo wadanda suka fito daga kananan hukumomin Kano 44 sabbin dabarun amfani da Injinin noma na zamani.
Kwamishinan ya ce, sun gayyato wani kamfani daga kasar Oman, kuma sun bai wa matasan kyautar Injin aikin noma na Power Tiller wadnda zai bai wa matasan gudanmawa a aikin noman su.
Kwamishinan, ya kara da cewa, gwamnatin Kano za ta kara sayo Injina da sauran kayan aikin gona a nan gaba, matukar wadanda suka ci gajiyar a wannan lokaci sun samar da sauyi, a harkokin noma.
You must be logged in to post a comment Login