Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano : An kama magungunan da aka haramta na naira biliyan 5

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta kama tare da lalata wasu miyagun kwayoyin da kudinsu ya kai kimanin naira biliyan 5 a wani aiki da suka yi a jiya a sassan  jihar nan 15.

Gwamna Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a jiya Talata a yayin da ake aikin kona wasu jabun kwayoyi da aka gudanar a harabar ofishin NDLEA.

Gwamna Ganduje wanda mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilce  ya ce yawan samun jabun kwayoyi na karuwa a jihar Kano, inda ya ce gwamnatin jihar Kano na iya kokarinta na magance matsalolin kwaya a jihar kano.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da sa hannun sakataren gwamna Hassan Musa Fagge .

Ya ce adadin kwayoyin da aka kwace tare da kona su kudinsu ya kai kimanin naira biliyan 5, inda ya ce a don haka ne suka zo domin ganin kayan da aka  kama.

Daga cikin akwai na kimanin naira miliyan 543 wanda aka haramta amfani da su.

Wasu magungunan kwari da manoma ke amfani da su na da illa ga lafiyar dan Adam

Hukumar CUSTOM: ta kama mota makare da maganin Codeine na kimanin naira miliyan 240

SACA: kimanin kaso 35 cikin dari masu dauke da cutar HIV ke karbar magani

Sanarwa ta kara da cewa an samu nasarar kama wadannan kwayoyi ne sakamakon hadakar kwamitin da aka hada na yaki da safarrar miyagun kwayoyi abinci da wa’adinsu ya kare da sauran abubuwan da aka haramta shigo da su.

Gwamna Ganduje ya ce kwamitin ya hadar da wasu daga cikin jami’an ‘yan sanda da  ‘yan Karota da ‘ yan Hisbah da wasu daga cikin kungiyar masu harhada magunguna da hukumar NAFDAC da  ma’aikatar sadarwa da hukumar lura da magunguna da sauran su.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!