Connect with us

Labarai

NAFDAC ta kama jabun magunguna

Published

on

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta sanar da kama wasu magunguna marasa inganci a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi wato kasuwar Sabon Gari dake kano.

Shugaban hukumar mai kula da shiyyar Jihar Kano Malam Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya talata, yayin holen magungunan, har ma da wasu da aka kama suna sayar da zuma mara inganci a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Hukumar NAFDAC ta kwace kwayoyi da jabun magunguna na Naira biliyan uku a Kano.

NAFDAC: ta gargadi jami’an lafiya da su kula da nau’in rigakafin amai da gudawa na bogi

Shaba Muhammad ya bayyyana cewa magungunan da aka kama din suna tattare da mummunar illa ga lafiyar bil’adama matukar aka yi amfani da su.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa hukumar ta ce za ta ci gaba da bincike don gano wadanda suka mallaki kwayoyin don gurfanar da su gaban Kotu, har ma ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da baiwa hukumar hadin kai don tona asirin bata-garin da ke gudanar da irin wannan muguwar sana’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!