Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

       Wadansu magidanta sun karbi  Musulunci a garin Sumaila       

Published

on

 

A yankin Sumaila dake garin Kano  hukumar Shari’ar  Musulunci tare da hadin gwiwar kwamitin yada addinin musulinci dake karamar hukumar Tudun Wada karkashin  jagorancin Malam Nasiru Alhassan sun  musuluntar da wani magidanci tare da matarsa dake gundumar Gani dake Sumaila  a yammacin  Talata .

Yayin da suke karbar Kalmar shahada sun nuna farin cikin su da godiya ga Allah [ SWT ] dangane da fahimtar gaskiya  tare da kuma kama  tafarkin tsira, kamar yadda  Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya koyar.

Mai gidan kamar yadda ya bayyana yace  duk abin da aka ce rabon mutum ne daga  ubangiji sai mutum ya  tarar da shiriyar Allah madaukakin Sarki.

Ya kara bayyana cewa, duk mutumin da yazo Duniya rayuwa ya kamata ya san makomar sa bayan mutuwar sa.

Magidacin ya nemi a san ya masa sunan  Marigayi Sheikh  Jaafar yayin da matar sa ma ta nemi a sa mata suna Hafsatu.

Shima a nasa bangaran, Malam Nasiru Alhasan yace  ya shafe tsawon shekaru yana yin da’awar  shigowar su musulunci kafin Allah ya fahimtar dasu  .

Malam Nasiru yace akalla  shekara 13  yana Da’awah amma kiran bai isa zuciyar su ba sai a yanzu.

Ya kara bayyana irin mu’amalantar su  da yayi ta abinci da tufafin su da ma Addinin su  duk saboda ribato zukatansu na tsawon  shekara goma sha uku.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!