Labarai
Gwamnatin Kano ta kuduri sabunta ginin Majalisar dokoki da gina Titina

Gwamnatin jihar Kano, bayyana shirinta na fara gudanar da aikin sabunta ginin zauren majalisar dokoki da kuma wasu ayyukan samar da titi mai tsawon kilomita Ashirin a karamar hukumar Makoda da wasu titunan a cikin kwaryar Birni.
Kwamishinan ayyuka da gidaje injiniya Marwan Ahmad, ne ya bayyana hakan, ta bakin Daraktan tsare-tsare da bincike na ma’aikatar ayyuka Injiniya Lawal Datti a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan taron ganawa da yan kwalgilar da ke takarar neman yin ayyukan.
Daya daga cikin masu neman Kwangilar ayyukan Garzali Muhammad Usman, wanda yayi magana a madadin sauran ‘yan kwangilar, ya bada tabbacin yin aiki mai inganci domin ci gaban al’ummar jihar Kano.
Ma’aikatar ayyukan, ta bukaci wadanda za su rabauta da kwangilar da su tabbatar sun yi aiki mai inganci kuma a kan lokaci.
You must be logged in to post a comment Login