Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Mun fara ginin ofishin ‘yan sanda a karamar hukumar Gwarzo – Dr. Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta dasa harsashin fara ginin ofishin ƴan sanda a Getso da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

Aikin wanda za a gudanar da shi a ƙanƙanin lokaci zai lakume sama da naira miliyan ɗari da sittin.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, lokacin da yake kafa harsashin ginin babban ofishin ‘yan sanda a tsohuwar tashar mota ta Getso.

Ya ce, za a gina babban ofishin ‘yan sanda kamar na kowacce Karamar hukuma, tare da ginawa babban baturen ‘yan sandan da za a kawo gida, da kuma gidajen manya da kananan jami’an yan sanda, wanda za a kammala cikin watanni 8.

Da yake bayani Daraktan kula da gine-gine a ma’aikatar ayyuka ta jihar Kano Injiniya Abdulkadir Salihi ya ce, “ma’aikatar mu za ta rika bibiyar aikin domin ganin anyi shi da inganci kuma a kan lokaci”.

Shi ma dan Kwangilar da aka bai wa aikin Alhaji Muhammad Halilu Getso ya ce, “Za mu tabbatar mun yi aiki mai kyau, kuma za mu gama akan lokaci cikin gaskiya da rikon Amana”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!