Labarai
Gwamnatin Kano ta kwace shaidar mallakar wasu gidaje a Kwankwasiyya da Amana

Gwamnatin jihar Kano, ta karɓe lasisin mallakar dukkan gidajen da ba a ci gaba da aikin ginin su ba a rukunin gidaje na Kwankwasiyya da Amana, bayan cikar wa’adin watanni biyar da ta bayar tun da farko.
Kwamishinan gidaje Arc. Ibrahim Yakubu Adamu Wudil, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da ya kira a Alhamis din makon nan.
Kwamishinan na harkokin Gidaje, ya kuma bayyana cewa za a rushe dukkan gidajen da aka gina ba bisa tsarin tasawirar da aka amince da ita ba, domin tabbatar da daidaito da ingancin gine-gine a biranen.
You must be logged in to post a comment Login