Labarai
Gwamnatin Kano ta musanta rahoton da cibiyar WSCIJ ta fitar

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da wani rahoton da cibiyar binciken ƙwaƙwaf a fannin aikin jarida ta Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism ta fitar, wanda ya nuna cewa Kano na daga cikin jihohin da ke kan kan gaba wajen cin zarafin ƴan jarida.
Kwamishinan yaɗa Labarai da wayar da kan jama’a Kwamrad Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a daren Larabar makon nan.
Kwamishina Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce rahoton bai yi adalci ba ga gwamnatin Kano, domin a cewar sa, gwamnatin Abba Kabir Yusuf tana bai wa ƴan jaridu cikakken ƴanci wajen gudanar da aikinsu ba tare da tsangwama ba.
Waiya Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na ganin kafafen yada labarai a matsayin muhimmin abokin aiki wajen isar da saƙo ga al’umma da kuma ƙarfafa mulkin dimokuraɗiyya.
Haka kuma Gwamnatin ta jihar Kano ta bukaci cibiyoyin da ke fitar da irin waɗannan rahotanni da su tabbatar da ingantaccen bincike kafin wallafa su.
A Talatar makon nan ne dai cikin ta bayyana cewa jihohin Lagos da Kano da kuma birnin tarayya Abuja ne kan gaba wajen cin zarafin ƴan jarida a faɗin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login