Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta musanta shigo da Corona ta Filin Jirgin saman Malam Aminu Kano

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rade-radin da aka wayi gari da shi yau cewa wai an samu wani mai dauke da kwayar cutar Corona a filin Jirgin saman Malam Aminu Kano.

Mataimakin shugaban kwamitin yaki da kwayar cutar Corona na Jihar Kano Farfesa Abdulrazak Habib ne ya sanar da hakan yayain zantawa da Freedom Radio ta wayar tarho a yau.

Wata majaiya ta shaidawa Freedom Radio cewa wani matashi ne mai shekaru 17 ya fara amai bayan sauka daga Jirgi da ya taso daga Jihar Lagos da safiyar yau, wanda kuma nan take aka killace shi.

Farfesa Abdulrazak Habib ya tabbatar da cewa duk wasu gwaje-gwajen lafiya da aka gudanar a kan matashin sun nuna cewa baya dauke da cutar, kuma an sallame shi.

Sai dai ya ce za su ci gaba da bibiyarsa, bayan da suka tattara bayanai a kansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!