Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta nuna takaici kan masu Adaidaita Sahu da ke karya dokar Sanitation

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta nuna takaici bisa yadda masu ababen hawa musamman ƴan Adai-daita Sahu suke karya dokar tsaftar muhalli.

Kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso, ne ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala aikin duban tsaftar muhalli na karshen wata da aka gudanar yau Asabar kamar yadda aka saba a sassan Kano.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso. ka kara da cewa an samu karancin zirga-zirgar jama’a da bude guraren kasuwanci, sai da kalubalen zirga-zirgar ababen hawa da aka samu musamman masu tuka baburan wadanda saka karya dokar.

Yayin duban tsaftar muhallin an ci tarar da wadanda suka karya doka nan take karkashin kotun tafi da gidanka.

 

Rahoton: Madina Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!