Kasuwanci
Gwamnatin Kano ta raba kayan koyon sana’o’i ga ƙungiyoyin Kofar Mata da Gwale

Gwamnatin jihar Kano ta raba kekunan dinki da sauran kayan aikin yin Takalma da jakunkuna na miliyoyin kudi ga kungiyoyin Kofar mata da Gwale a kokarinta na magance matsalar rashin aikin yi da kuma ayyukan daba a tsakanin matasa.
Da ya ke mika kayan a yau Talata, kwamishinan ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da Kirkire-kirkire Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya bukaci sauran unguwanni da su rika samar da cibiyoyin koyar da sana’o’i ga matasa domin su ma su ci gajiyar irin tallafin.
Kwamishinan, ya kara da cewa, manufar gwamnati ta bayar da kayan shi ne domin ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na samar wa matasa ayyukan yi.
Haka kuma ya kara da cewa “ A baya wurin da aka gina cibiyar koyar da sana’o’in a kofar Mata waje ne da ya kasance matattarar bata gari, amma yanzu Alhamdulillahi bisa jajircewarmu yanzu gashi an kwato wajen daga hannun mutanen da suka mallake shi ba bisa ka’ida ba.”
Kwamishina Dakta Yusuf Ibrahim Kofar mata, ya bayyana cewa gwamnatin Kano za ta tallafa wa duk wata kungiya da tasamar da cibiyar koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai da dukkan kayan aikin da ake bukata.
A nasa bangaren, Malam Ali Musa Kofar Mata mataimakin shugaban Kungiyar Inuwar Kofar Mata, ya bayyana godiya ga gwamnatin jihar Kano da kuma ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da Kirkire-kirkire bisa raba musu kayan ya na mai cewa za su taimaka matuka wajen kara yawan daliban da suke dauka don koyar da su sana’o’i.
Shi ma babban Maga-takardan kungiyar Safinatul Khairi da ke unguwar Gwale Malam Bashir Barau, ya bayyana farin cikinsa bisa karbara kayan inda ya ce, za su tabbatar da cewa sun yi amfani da su yadda ya dace wajen koyar da sana’o’in Dogaro da kai ga matasa maza da mata.
You must be logged in to post a comment Login