Connect with us

Labarai

Yadda kwamitin magance daba ya kai samame Ramin Research a Kano

Published

on

Kwamitin da Gwamnatin Kano ta kafa na magance ayyukan Daba da shaye-shaye da kuma dawo da zaman lafiya, ya cafke fiye da matasa 50 a wani samame da ya kai Ramin Research da ke unguwar Rimin Kebe da yammacin ranar Asabar.

Kwamitin karkashin jagorancin shugabansa Dakta Yusuf Ibrahim Kofar mata, ya kai samamen ne tare da rakiyar jami’an tsaro na Ƴan Sanda da DSS da Civil Defence da na hukumar NDLEA da takwararta ta yaki da fasa-kwauri da jami’an gidan gyaran hali yan Bijilante da rundunar yaƙi da kwacen waya da sauransu.

Da ya ke jawabi ga manema labarai, kwamishinan ƴan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori,  ya bayyana cewa sun samu nasarori da dama a aikin inda aka kama mutane 51 a ramin na Research wanda ya daɗe ya na bada gudunmawa wajen lalata tarbiyyar matasa.

Haka kuma, ya ce, “Ko da iya haɗuwarmu a yau wajen gudanar da wannan aiki babbar nasara ce, tunda ga mu yan sanda da sauran jami’ai irin su  DSS da Civil Defence da na hukumar NDLEA da na hukumar yaki da fasa-kwauri da jami’an gidan gyaran hali yan Bijilante da rundunar yaƙi da kwacen waya, wannan ma babbar nasara ce.”

” Muna kira ga iyaye, da su riƙa kula da ƴaƴan su tare da tabbatar da cewa ba su fada cikin wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye ba,” in ji kwamishinan.

A nasa ɓangaren, Kwamandan hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA shiyyar Kano, Abubakar Idris Ahmad, ya bayyana cewa, cikin kayan maye da suka cafke yayin samamen sun hadar da miyagun ƙwayoyi da tabar Wiwi da ruwan sinadarin Codiene da sauran  kayan maye.

Ya ƙara da cewa, bayan samun wannan kayan mayen, tuni jami’an mu sun fara aikin tantance su kuma da zarar an kammala tantancewa za mu sanar da adadin su kuma mu miƙa su ga kotu.

Alhaji Shehu Muhammad Rabi’u, shi ne shugaban kungiyar Sintiri ta Vigilante na Kano, ya bayyana jin dadi bisa yadda aka kai samamen, ya na mai cewa, A baya Ramin na Research ba ya shigowa sakamakon yadda bata gari suka mayar da shi babbar mafaka.

Haka kuma, ya ce, idan jami’an tsaro suka shiga wurin suna fuskantar matsaloli daga ƴan unguwar inda a lokuta da dama suke yi musu ihu.

Shi kuwa, shugaban kwamitin Dakta Yusuf Ibrahim Kofar mata, cewa ya yi gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya kafa kwamitin domin tsaftace Kano daga ayyukan Daba da kuma dawo da zaman lafiya.

Kwamishinan ya kuma ja kunnen duk masu son tada fitina a Kano da kuma masu sha da dillancin kayan maye da su kauce wa yin hakan don kauce wa fushin mahukunta.

Wasu daga cikin mazauna unguwar ta Rimin Kebe da ke makwabtaka da ramin, sun bayyana jin dadinsu bisa kai samamen inda suka ce an sha yin kisa a wurin, kuma ba su da cikakken kwanciyar hankali sakamakon ayyukan ta’addanci da ake yi a yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!