Labaran Kano
Gwamnatin Kano ta sake salo wajen kubutar da yaran Kano
Gamayyar Kungiyoyin rajin kare hakkin al’umma a jihar Kano sunyi kira da babbar Murya ga gwamnatin Kano data kara kaimi wajen ganin ta kubutarda sauran yaran da aka sace domin dawo dasu cikin iyalansu.
Sakataren Gamayyar Kungiyoyin na Jihar Kano Injiniya Bashir Adamu Aliyu ne ya bayyana hakan lokacin taron da kungiyoyin suka shirya domin duba lafiyar iyayen yaran da basu magun guna kyauta tare da basu shawarwari ta fuskar shari’ah.
Bashir Adamu Aliyu ya kuma kara da cewa abun takaicine a cigaba da zuba idanu ana cigaba da satar kananan yara a Kano tare da canza musu addini , a don haka ya zama wajibi gwamnati ta kara matsa kora domin gano ko su waye.
Da take nata Jawabin a yayin taron Barista Sadiya Adamu Aliyu cewa tayi adadin yaran da aka sace ya karu don kuwa izuwa yanzu sama da iyayen yara dari ne suka shigar musu da korafin cewa an sace musu yaran su.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito iyayen yara da dama ne suka halarci taron daga unguwanni daban daban wadanda aka sacewa yara sun kumayi fatan gwamnati ta yi gaggawar gudanarda buncike domin gano sauran yaran su da aka sace sakamakon mawuyacin halin damuwar da suke ciki.