Labarai
Gwamnatin Kano ta sha alwashin cigaba da yaki da cin hanci da rashawa
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, gwamnatin sa za ta ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a matsayin wata hanya ta samar da ci gaba a Jihar, wanda hakan zai daidai da manufar gwamnatin tarayya ta fatattakar cin hanci da rashawa tsakanin ma’aikatan gwamnati da daidaikun kasar nan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban ma’aikatan jihar Kano, Muhammad Awwal Na’iya yayin taron bikin yaye daliban makarantar koyon aikin yaki da cin hanci da rashawa dake birnin Keffi na jihar Nasarawa.
Muhammad Awwal Na’iya ya kara da cewa, aikin yaki da cin hanci da rashawa aiki ne da ke bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci a kowanne matakai domin kawo karshen al’amarin, don tabbatarwa tare da gudanar da gwamnati mai tsafta.
Da yake tsokaci a yayin taron shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Malam Muhyi Magaji Rimin Gado jaddada kudurin sa yayi na samar da wata cibiya da za’a rika baiwa ma’aikatan hukumar horo da kuma kayayyakin aiki na zamani da za su taimaka musu yayin gudanar da ayyukan su.