Labarai
Gwamnatin Kano Ta Sha Alwashin Inganta Jin Daɗin Ma’aikata

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudirinta na ci gaba da inganta rayuwar ma’aikata da samar musu da yanayin aiki nagari a fadin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a bikin Ranar Ma’aikata da aka gudanar da safiyar yau Alhamis, a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, Kano.
Gwamnan ya ce gwamnatin sa na daukar matakai na horar da ma’aikata tare da samar da kayayyakin aiki na zamani domin sauƙaƙa aikinsu da ƙara musu kwarewa.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen Jihar Kano, Kwamared Kabiru Inuwa ya bukaci gwamnan da ya cika alkawarin da ya dauka na gina ɗakin taro a sakatariyar ƙungiyar, tare da sanya sunan Marigayi Muhammadu Abubakar Rimi.
You must be logged in to post a comment Login