Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta shirya kwashe matan da ke ƙasa gada

Published

on

Daga: Zainab Aminu Bakori

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala shirin yaki da matan da ke baro gidajen su suna kwanan a karkashin gada da bakin hanyoyi don gudun fadawarsu cikin hatsari.

Kwamishiniyar mata da walwalarsu Malama Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Redio.

Ta ce a yanzu sunyi shiri tsaf domin ci gaba da kamen mabarata da kuma matan da ke baro garuruwansu su shigo Kano suna kwana a karkashin gada da kuma barace-barace.

Malama Zahra’u Muhammad ta kuma ce, maukar hukumar su ta kama irin wadannan mata tana saurarar kokensu tare da bas u tallafin jario don su koma garuruwan su suyi sana’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!