Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta tabbatar da Alhaji Shehu Rabi’u a matsayin shugaban rundunar bijilanti

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da Alhaji Shehu Rabi’u a matsayin sabon kwamandan rundunar bijilanti.

Wannan na zuwa ne bayan cika kwanaki 58 da rasuwar babban kwamandan rundunar Muhammad Kabir Alhaji da aka fi sa ni da M K ALHAJI.

Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano Murtala Sule Garo ne ya mika masa takardar shaidar kama aiki a jiya Talata,jim kadan da .ika masa takardar Alhaji Shehu Rabi’u yayi karin bayani kamar haka.

A nasa bangaren gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo ya wakilta ya ce, shugaban ya cancanci bashi ragamar jagorancin rundunar.

Tun a baya dai Alhaji Shehu Rabi’u ya rike mukamin mataimakin mwamandan sashen kula da ayyuka na Musamman.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!